’Yan Sandan a Jihar Yobe sun ce wasu da ake zargin ’yan kungiyar Boko Haram ne sun sake lalata wasu layukan wutar lantarki mai karfin 330 KVA, lamarin da ya jefa mazauna jihohin Yobe da Borno cikin halin duhu kamar yadda ya faru a watannin baya.
Aminiya-trust ta rawaito cewa, Kakakin rundunar, Dungus Abdulkarim ya shaida wa ’yan jarida cewa maharan sun yi amfani ne da abubuwan fashewa wajen lalata turakun da suka dauko wutar lantarkin daga Gombe zuwa jihohin Yobe da Borno.
- Zulum Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Kasuwar Banki Da Rikicin Boko Haram Ya Ɗaiɗaita
- Harin Boko Haram Ya Yi Ajalin Mutane 7 A Yobe
Ya ce “Wadannna turakun wutar lantarkin suna nan ne a kusa da kauyen Kasaisa da ke Karamar Hukumar Damaturu a Jihar Yobe.
“Wannan barna ta lalata turakun da ke dauke da wayoyin samar da hasken wutar lantarkin ya jefa mazauna jihohin biyu cikin duhu,” in ji shi.
Harin da aka kai kan layukan lantarkin shi ne hari na biyu cikin watanni uku.
Mahara sun lalata su a watan Disamba, amma aka gyara a watan Janairu, kafin yanzu da aka sake lalata su.