‘Yandaba sun farmamki tawagar dan takarar Sanatan APC na kano ta tsakiya Abdulsalam Abdulkarim Zaura, a yammacin ranar Asabar a Gadar Katako da ke unguwar Rimin Kebe a cikin garin Kano, mutane 17 wadanda harin ya rutsa da su suna asibiti suna jinya.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, arangamar da aka yi an samu zubar da jini a yankin da ke da mazauna da dama a kwaryar garin Kano.
Zaura wanda ya bayar da cikakken bayani kan harin a shafin sa na Facebook da aka tabbatar ya bayyana cewa yana dawowa daga ziyarar ta’aziyyar rasuwa a unguwar Gayawa ne aka kai wa ayarinsa hari.
Zaura ya bayyana cewa, “Da yammacin yau (ranar Asabar), muna dawowa daga ziyarar ta’aziyyar marigayi Hakimin Gayawa a karamar hukumar Ungogo da ke kusa da Gadar Katako ta Rimin Kebe, da ke iyaka da kananan hukumomin Nassarawa da Ungogo, wasu ‘yandaba sun kai wa ayarin mutanena hari, akwai mutane masu kanana da manyan rauni akalla 17 dake jinya yanzu haka a Asibiti.”