Wasu ‘yan bindiga sun afka kan wasu manoma sun kashe hudu daga cikinsu tare da yin garkuwa da wasu mutum takwas daga kauyen Nahuta da ke karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina a ranar Asabar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Abubakar Aliyu, ya tabbatar da faruwar kai harin ranar Lahadi a Katsina.
- ‘Yansanda Sun Kashe ‘Yan Bindiga 13, Sun Ceto Mutane 268 A Katsina
- ‘Yansanda Sun Kashe Shugabannin ‘Yan Ta’adda 3 A Jihar Katsina
Batsarin ya ce manoman suna girbin amfanin gonakinsu ne a lokacin da maharan suka far musu.
Daya daga cikin manoman da suka yi nasarar tserewa yayin kai harin sun samu raunuka sakamakon harbin ‘yan bindigar.
Ya kara da cewa, “Wadanda ake zargin ‘yan fashin daji ne suka far wa manoman, inda suka bude musu wuta suka kashe hudu tare da raunata daya; sun kuma yi awon gaba da wasu takwas,’’ cewar Aliyu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp