Tsohon shugaban asibitin kwararru da ke Kano, Dakta Kabiru Abubakar ya bayyana cewa ‘yan jarida na da rawar takawa wajen dakile matsalar karancin kayan aikin kula da cutar daji, domin babu wanda ya fi ‘yan jarida samun damar na fadakar da shugabanni da kuma al’umma kan matsalolin da suka addabi mutane kuma ta hanyar ayyukansu za a iya warware duk wata matsala da ta kunno.
Dakta Kabiru ya bayyana haka ne a lokacin taron likitoci masu neman sanin makaman aiki da ya gudana a Kano.
- Shugaba Xi Ya Tattauna Da Manyan Jami’an Gudanarwar Yankunan Hong Kong Da Macao
- CMG Ya Gabatar Da Tambarin Musamman Da Kayan Murnar Bikin Bazara Na Kasar Sin Na Shekarar 2023 Mai Alamar Zomo
Taro ya samu halartar dimbin masana daga asibituci da cibiyoyin lafiya a dukkanin sassan kasar nan.
Har ila hau, ya ce a lokacin da ya samu dama ya yi amfani da ita wajen horar da likitoci da dama a kan fannonin da ya shafi larurar laka, kashi, cututtukar kafa, da dai sauran, wanda yanzu haka likitoci a fanni na kashi da laka kashi 60 cikin 100 da suke Nijeriya daga asibitin Dala suka samu wannan horo.
Ya nuna farin cikinsa da wannan nassara ta horar da masu gadon sa a aiki. Haka kuma ya shawarci likitoci masu tasowa da su tsaya su yi aiki yadda ya kamata, domin ta haka ne ake samun biyan bukata da daukaka a duniya da lahira.
Haka kuma ya ce abubuwan da su yake tunawa na nasarori a rayuwarsa da kuma shugabancin da ya yi su na da yawa, musammam irin ci gaban da aka samu a wannan asibiti.