Wasu daga cikin mazauna jihar Bauchi sun yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan amincewa da cigaba da amfani da tsohuwar takardar N200 har zuwa ranar 10 ga watan Afrilun 2023.Â
A safiyar ranar Alhamis ce, Shugaba Buhari a jawabinsa ga ‘yan Nijeriya ya sanar da wannan matakin, inda ya umarci babban bankin Nijeriya CBN da ya bayar da tsoffin takardun N200 ga jama’a don cigaba da amfani da su har zuwa ranar 10 ga watan Afrilun 2023.
Wasu daga cikin ‘yan jihar, Mercy Emmanuel da mista Japhet Audu da Malam Sani Saminu da sauransu, sun godewa shugaban kasar kan daukar wannan matakin.
Haka kuma, sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da wadatattun takardun kudaden, musamman don rage wa ‘yan kasar bin dogon layi wajen na’urar sarrafa kudi (ATM).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp