Akalla mutane 27 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin kwale-kwale da ya afku a Gbajibo da ke karamar hukumar Kaiama a jihar Kwara.
LEADERSHIP ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a lokacin da ‘yan kasuwar ke dawowa daga jihar Neja inda suka je wata kasuwa mai ci mako-mako.
- Birtaniya Ta Fitar Da Sabbin Tsauraran Dokokin Zama A Ƙasar
- Gidan Adana Kayayyakin Tarihi Na Amurka Ya Mayarwa Kasar Sin Rubuce-rubucen Hannu Masu Daraja Na Lokacin Yake-yake A Kasar
Wani da ya tsira da ransa, ya dora alhakin faruwar lamarin a kan makare Kwale-kwale da kayan da ya fi karfinsa a dare.
Shugaban karamar hukumar Kaiama, Honarabul Abdullah Danladi ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Lahadi yayin wata tattaunawa da LEADERSHIP ta wayar tarho.
Danladi ya ce ya jagoranci tawagar gwamnati domin jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa.
Ya kara da cewa, gwamnati za ta kafa wani kwamiti wanda za a dora masa alhakin tilasta wa fasinjojin jirgin ruwa yin amfani da rigar tsira don dole.
Danladi ya ce gwamnati za ta kuma dakatar da tafiye-tafiye da daddare a wani bangare na matakan kawo karshen yawaitar haduran Kwale-kwale da ake fama da shi a yankunan da ke zagaye da ruwa.
Shi ma mai martaba Sarkin Kaiama, Alh Muazu Omar ya nuna alhininsa kan wannan lamari da ya faru.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp