Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana cewa wasu manyan ‘yan kasuwa daga kasar Amurka sun nuna sha’awarsu ta zuba jari a jihar Nasarawa, yana mai cewa, hakan zai samar da ayyukan yi ga matasa marasa aikin yi a fadin kananan hukumomi 13 na jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran gwamnan jihar, Ibrahim Adra, a garin Lafia babban birnin jihar Nasarawa.
- NAF Ta Tarwatsa Wani Sansanin ‘Yan Ta’adda A Kaduna
- Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Ya Ce Babu Rashin Fahimta Ko Shubuha Dangane Da Kuduri Mai Lamba 2758
Gwamna Sule wanda ya ziyarci Amurka domin jan hankalin masu zuba jari, ya bayyana cewa, masu zuba jarin sun nuna sha’awar zuwa jihar domin zuba jari a fannonin noma, hakar ma’adinai, ilimi, gina gidaje, mai da iskar gas da kuma kiwon lafiya.
Mun rahoto cewa, gwamna Sule ya tafi kasar Amurka ne daga Abuja a ranar 15 ga watan Satumba bisa gayyatar cibiyar Woodrow Wilson da ke Washington DC da kuma UN SDG da ke New York.
An jiyo Shugaban Hukumar Bunkasa Zuba Jari ta Jihar Nasarawa (NASIDA), wanda ya je Amurka tare da Gwamnan yana cewa, “Sha’awar yin kasuwanci a Jihar Nasarawa ta bunkasa ta bangarori da dama inda ‘yan kasuwar suka nuna sha’awar zuwa Nasarawa domin zuba jari a karkashin jagorancin Gwamna Sule.”