A wannan makon ne ‘yan majalisar dokoki na kasar Sin, za su tattauna kan daftarin gyare-gyare ga dokokin kasar, matakin dake nuna karfin kafa dokoki da sanya ido kan kundin tsarin mulki.
Mai magana da yawun hukumar kula da harkokin majalisar dokoki ta zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Zang Tiewei, ya bayyana cewa, manufar daftarin gyare-gyaren, ita ce kyautata tsari da samar da kyakkyawan hadin kai tsakanin shawarwarin da ‘yan majalisar suka gabatar da yin gyare-gyare.
Zang ya bayyana cewa, gobe Laraba ne za a mikawa wani zama na zaunannen kwamitin NPC daftarin kwaskwarimar don yi masa karatu na farko.
Bugu da kari, matakin zai inganta tsarin dokoki da aikin majalisa da zaunannen kwamitinta, da kara abubuwan da suka dace don biyan bukatun sake fasalin tsari na sanya ido, da ma inganta abubuwan da suka dace na dokoki da ka’idoji na dokokin cikin gida da kara sake nazartar takardun da aka saba bisa al’ada. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp