Majallisar Wakilai ta yi kira ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da ya kara daukar matakai domin kubutar da fasinjojin 51 da ‘yan bindiga suka sace a jirgin kasan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna.
‘Yan majalisar sun roki shugaban da ya dauki matakai don a kubutar da sauran wadanda ‘yan bindigar suke ci gaba da rikewa a daukacin fadin kasar nan.
- SEMA Ta Raba Wa ‘Yan Gudun Hijira Kayan Abinci A Jihar Borno
- An Kashe ‘Yan Bindiga 4 Da Cafke Matar Da Ke Kai Wa ‘Yan Ta’adda Makamai A Kaduna
Kazalika, Majilsar ta yi kira da gwamnatin tarayya da ta kafa wani kwamiti mai karfi da zai taimaka wajen kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su a fadin Nijeriya.
Kiran na ‘Yan Majalisar ya biyo bayan wani kudurin da ‘yan majalisar da suka hada da Bamidele Salam da Julius Ihonvere da Mansur Manu Soro da kuma sauran ‘yan majalisar bakwai suka gabatar wa a zauren majalisar.
Mambobin sun ce, idan har ba a ceto wadanda aka sace din ba, hakan zai sa ‘yan Nijeriya su fidda rai daga wannan gwamnatin.