• English
  • Business News
Saturday, October 18, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yan Mata Mu Yi Karatu Sannan Mu Kama Sana’a – Khadija Sambo

by Bilkisu Tijjani
1 year ago
Mata

KHADIJA SAMBO wata matashiya ce, wacce kasuwanci yake ba ta sha’awa idan ta ga mata ‘yan uwanta suna yi suna taimaka wa kansu da iyayensu. A kan hakan ne ta shawarce su da su yi karatu sannan kuma su kama sana’a domin dogaro da kai, kamar dai yadda za ku ji a cikin wannan tattaunawarsu da BILKISU TIJJANI KASSIM.

Da fari za mu so sanin cikakken sunanki da tarihinki?

Sunana Khadija Sambo Lawan ni haifaffiyar Hadejia ce na taso a Garin Hadejia na yi karatuna a Garin Hadejia.

Shin Khadija matar aure ce?

A a bani da aure muna dai sa rai in sha Allahu, kuma ni ‘yar kasuwa ce

LABARAI MASU NASABA

Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?

Ko Kin San… Dalilin Da Ke Sa Mata Ke Ganin Farin Ruwa Kafin Ko Bayan Al’adarsu?

Wanne irin kasuwanci kike yi?

Eh ina saida abubuwa da dama

Me ya ja hankalinki har kika shiga wannan kasuwanci?

Abin yana bani sha’awa idan na ga mata ‘yan uwana suna kasuwanci, sannan kuma suna taimaka wa kansu da iyayensu shi ne ya ja hankalina

Mene ne matakin karatunki ba?

Yanzu ajina biyu a jami’a

Wanne irin matsaloli kike fuskanta cikin wannan kasuwanci naki?

Matsalolin dai su ne akwai lokacin da aka turo min kaya a waya zan sara, sai bayan na sa an kawo min sai na ga ba kamar wanda na gani a waya ba.

Zuwa yanzu wanne irin nasarori kika cimma?

Gaskiya na cimma nasarori da dama na taimaka wa kannena wajen karatuna taimaka wa iyaye da ‘yan uwa da sauran mutane wannan ma nasara ce babba.

Wanne abu ne ya fi faranta miki rai game da sana’arki?

Abin da ya fi faranta min rai shi ne abubuwan da suka fi karfina a da yanzu na fi karfinsu a dalilin sana’ata

Ta wacce hanya kike bi wajen tallata sana’arki?

Ta yanar gizo-gizo kamar WhatsApp, Facebook, Insgram, da dai sauransu.

Da me kike so mutane su rika tunawa da ke?

Ina so mutane su rika tunawa da ni a kan Jajircewata a kan sana’ata

Wacce irin addu’a ce idan aka yi miki kike jin dadi?

Mata

Idan aka ce Allah ya yi wa rayuwata albarka, saboda wannan addu’ ar ta hada da komai ina jin dadi sosai

Wanne irin goyon baya kike samu daga wajen iyaye da ‘yan uwanki?

Gaskiya Ina samun goyan baya sosai suna karfafamin gwiwa akan karatuna da kasuwancina sosai babu abin da zan ce musu sai addu’a da fatan alkhairi

Kawaye fa?

Ba ni da kawaye gaskiya

Me kika fiso acikin kayan sawa da kayan kwalliya?

Kayan sawa nafison atamfa kayan kwalliya hoda

A karshe wanne irin shawara za ki ba ‘yan uwanki mata?

Ina ba wa ‘yan uwana mata shawara a kan mu yi karatu sannan mu koyi sana’a koda a ce mun kammala karatu babu aikin yi za mu iya rike kanmu da sana’armu mu taimaki kanmu da al’umma baki daya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?
Adon Gari

Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?

October 12, 2025
tusar gaba
Adon Gari

Ko Kin San… Dalilin Da Ke Sa Mata Ke Ganin Farin Ruwa Kafin Ko Bayan Al’adarsu?

August 31, 2025
Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa
Ado Da Kwalliya

Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

August 3, 2025
Next Post
Xi Jinping Ya Kama Hanyar Zuwa Faransa Da Serbia Da Hungary Domin Ziyarar Aiki

Xi Jinping Ya Kama Hanyar Zuwa Faransa Da Serbia Da Hungary Domin Ziyarar Aiki

LABARAI MASU NASABA

Iwobi Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Firimiya

Iwobi Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Firimiya

October 18, 2025
Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI

Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI

October 18, 2025
An Fara Yi Wa Yara Miliyan 1.6 Rigakafi A Taraba

An Fara Yi Wa Yara Miliyan 1.6 Rigakafi A Taraba

October 18, 2025
Lewandowski Ba Zai Buga Wasan El Classico Ba

Lewandowski Ba Zai Buga Wasan El Classico Ba

October 18, 2025
Ƴansanda Sun Kama Gungun Masu Sojan Gona Suna Aikata Laifuka A Kano

Ƴansanda Sun Kama Gungun Masu Sojan Gona Suna Aikata Laifuka A Kano

October 18, 2025
Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴansanda, Sun Kashe 2 A Kaduna

Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴansanda, Sun Kashe 2 A Kaduna

October 18, 2025
Radda

Gwamnan Katsina Ya Bukaci Al’umma Su Hada Hannu Da Gwamnati Wajen Kawar Da Matsalar Tsaro

October 18, 2025
Yajin Aikin ASUU: Majalisar Dattawa Ta Tsoma Baki, Za Ta Gana Da Ministan Ilimi

Yajin Aikin ASUU: Majalisar Dattawa Ta Tsoma Baki, Za Ta Gana Da Ministan Ilimi

October 18, 2025
IMF

Fitar Da Kudi Ta Haramtacciyar Hanya Na Kara Dagula Matsalar Tattalin Arziki – IMF

October 18, 2025
majalisar kasa

Majalisar Wakilai Ta Gayyaci CBN Da Bankuna Kan Cire Wa Kwastomomi Kudi Ba Dalili

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.