Misali, ka dau lokaci kana neman aiki a wata ma’aikata. Kullum cikin bibiya ka ke yi, kana neman wanda za ka yi kamun kafa da shi. Kana ta addu’a, kana bin sahun takardunka da ka gabatar na neman wannan aikin; musamman saboda irin mugun bahagon bugun da talauci yake yi maka, ga matsatsi na rayuwa, kuma ga shekaru sai tafiya suke yi.
Kwatsam! Watarana sai aka kira ka a waya, aka sanar da kai cewa, gobe ka zo intabiyu don samun gurbin aikin da ka dauki shekara biyar kana bibiya. Ka wayi gari, daga kai sai Naira 100, iyaka kudin da zai kai ka zuwa ma’aikatar, tafiyar kilomita 30. Saboda irin kaunar da ka ke yi wa wannan aikin, ya sa ka hakura da abinci don ka biya kudin mota.
Karfe 9:00 na safe aka baka don fara intabiyu. Mintuna 20 za su kai ka Ma’aikatar daga unguwarku, amma ka fita tun karfe 8:00 na safe saboda gudun tsautsayi. Kuna hanya, kun ci rabin tafiya sai motar hayar da ka shiga ta fara shakewa, alamun matsala.
A zuciyarka kana ta addu’ar Allah Ya takaita matsala, saboda agogo na nuna karfe 8:20. Abin da ake gudu ya afku, mota ta tsaya cak, ta dau mugun zafi, tana fitar da hayaki. Direba ya tsaya, ya fito yana ta doka salati.
Kai ne mutum na farko da ya fara fitowa daga motar, ka samu direba kana son jin mene ne matsalar. Direba bai da amsa, saboda sai ya bude gaban motar sannan zai san me ke damunta. Kana bude baki ka ce, ‘Direba, bani kudin da zai kai ni inda za mu je’.
Direba tuni ya sha fetur da duka kudaden fasinja. Tun kana cijewa, kana danne damuwarka, amma kana duba agogo ka ga karfe 8: 50 na safe sai hankalinka ya tashi, ka firgita, lamarin ya harzukaka tare da jefaka cikin takaici.
Wannan harzukawa mai ban takaici ita ce ‘frustration’ – lamari ne na ban takaici me jefa mutum cikin damuwa, saboda yana fuskantar wani tarnaki da ke son hana shi cimma burinshi. Wancan misalin na sama, ya nuna mana yadda lalacewar motar haya ta jefa mutum cikin takaici saboda za ta shiga tsakaninshi da babban burin rayuwarsa.
Wannan mutumi saboda takaici da harzuka zai iya rufe direban motar nan da bugu. Wannan abin takaici ‘Frustration’ a nan ya rikida ya zama fushin da zai tunzura mutum ga aikata keta. Keta ‘Aggression’ anan aiki ne da zai iya zama cutar wa ga wani, wanda kuma a mafi yawan lokuta takaici me tattare da fushi ke haifar da shi.
Kenan a nan mun fitar da yanayi guda biyu wanda ya yi mana bayanin ‘Frustration-Aggression’, ma’ana dai takaici cikin fushi shi ne ke haifar da aikata keta. Wannan wani ra’i ne a kimiyyar zamantakewa wanda masana halayyar dan adam Dollar, Doob, Miller, Mower, da Sears suka samar a shekarar 1939 a littafinsu mai suna ‘Frustration and Agression’.
Wadannan masana sun ce, idan abin takaici ya sameka alhali kana gab da cimma burinka, ya fi ban haushi da harzukawa, wanda shi ya fi komi jefa mutum ga aikata keta.
Lokacin da Baba Buhari yake yakin neman zabe a shekarar 2014, bayan an samu hadewa tsakanin jam’iyyarsa ta CPC da ACN ta Yarbawa, da yawan ‘yan Nijeriya sun tsunduma cikin murna. Saboda kowa ya gaji da halin da ake ciki.
Da yawan ‘yan Nijeriya sun kudurci aniyar za su yi duk me yiwuwa don ganin nasarar Baba Buhari, wannan ne ma ya sa aka yi ta tura mishi kudi a asusun bankinsa na First Bank, wasu kuma suka tabbatar da wannan ra’ayin nashi na ‘a kafa – a tsare’.
Bayan Baba Buhari ya ci zabe, da yawan mutane, musamman talakawa suna kullace da burin samun ingantacciyar rayuwa nan kusa, ma’ana a cikin 2015 ma komi zai canza, idan an dau lokaci kafin dadi ya zo shi ne a shiga farkon 2016.
‘Yan kasuwa suna ta tsalle za a magance matsalar tsaro, don kasuwancinsu ya yalwata. Matasa sun shirya za su yi aure, dalibai suna ta murna za su kammala makaranta ba tare da yajin aikin ASUU ba. Wadanda suka kammala karatu sun kosa a rantsar da Baba don su samu ayyukan yi. Su kuwa magidanta, kowa ya wanke tukunya saboda za a sha jar miya da shinkafa.
Wannan kwallafa rai na tsammani da kyautata wa Baba Buhari zato ya jefa mafi yawan ‘yan Nijeriya cikin takaici, musamman da ta bayyana ga kowa cewa, ba fa za a sha jar miya ba. Ba za a iya samar da tsaro ba. Dalibai sun fi kowa galabaita, saboda ba ma batun kawo karshen yajin aiki ba, idan ka sa wa Baba Buhari wuka bai san cikakken ma’anar ‘ASUU’ ba.
Wannan takaicin da mutane ke ciki yana daya daga cikin dalilan da ya sa aka samu yawan maketata a cikin al’umma a yau. Labarai marasa dadin ji a tsakanin iyalai, ‘yan uwa, makwabta, abokai da sauransu. Saboda kowa cikinshi cike yake da takaicin da Baba Buhari ya kumsa mishi. Keta ta ko ina a cikin al’umma.
Shi kuma a na shi bangaren, Baba Buhari na huce nashi takaicin – takaicin gazawar gwamnatinsa ta hanyar ketar yin kunnen uwar shegu da duk wani surutu da ake yi.
Idan abin takaici da tashin hankali ya faru, sai ya haye jirgi ya bar kasar, wannan ma wani salo ne na keta saboda tsabar takaici da jin kunya.