Kungiyar kwadago ta kasa (NLC), ta umarci ma’aikata da su kauracewa yin amfani da layukan sadarwa na MTN da Airtel da Glo a sakamakon ƙarin kuɗin da suka yi na kashi hamsin cikin ɗari na kiran waya, sakon karta-kwana da Data.
A wata takardar bayan taro da ƙungiyar ta fitar wanda ta gudanar ranar Talata, kuma aka rabawa manema labarai a ranar Laraba, kungiyar ta shawarci ‘yan Nijeriya da su fara kauracewa kamfanonin daga gobe Alhamis da misalin ƙarfe 11 na safe.
- ‘Yan Nijeriya Za Su Maka Gwamnati A Kotu Kan Karin Kudin Kiran Waya
- NCC Ta Amince Da Ƙarin Kuɗin Data Da Kiran Waya
Sanarwar ta bukaci janye ƙarin farashin da komawa tsohon farashi har zuwa lokacin da kwamitin da ƙungiyar ta kafa ya kammala gudanar da tattaunawa tare da cimma matsaya.
Ƙungiyar ta kuma buƙaci ma’aikatan Nijeriya da sauran ‘ƴan ƙasa da su ƙaurace wa kiran waya ko amfani da datar kamfanonin MTN da Airtel da Glo a kowacce rana daga ƙarfe 11:00 na safe zuwa ƙarfe 2:00 na rana na kowace rana har zuwa ƙarshen watan Fabrairu.
NLC ta kuma soki Gwamnatin tarayya bisa gazawarta wajen kare muradun ‘yan kasa, inda ta umarci ‘ƴan Nijeriya da su daina sayen data daga kamfanonin.
Ƙungiyar na buƙatar kamfanonin su dawo wa Nijeriya da kuɗaɗen da suka kwashewa ‘ƴan ƙasa.
Kamfanin sadarwa na MTN ya fara amfani da sabon tsarin ƙarin kudin awanni kaɗan bayan da majalisar wakilai ta kasa ta bukaci gwamnati da ta dakatar da ƙarin.