Adadin ‘yan Nijeriya miliyan 1.63 daga cikin mutum miliyan 1.8 da a halin yanzu suke dauke da cutar kanjamau da ake kira da ‘Antiretrobiral’, a cewar hukumar yaki da cutar kanjamau ta kasa (NACA).
Darakta janar na hukumar NACA, Dakta Gambo Aliyu shi ne ya shaida hakan lokacin da ke ganawa da ‘yan jarida kan bikin tunawa da masu dauke da cutar kanjamau (AIDS) ta duniya, inda Nijeriya ke mataki na biyu a yawan masu dauke da cutar.
- Xi Ya Bukaci A Tsagaita Bude Wuta Tare Da Gudanar Da Tattaunawar Zaman Lafiya Kan Rikicin Falasdinu Da Isra’ila
- An Haramta Shan Sigari A Wuraren Shakatawa Da Makarantu A Faransa
A cewar Aliyu, Nijeriya kamar sauran kasashe na kan kokarin yaki da cutar kanjamau, ya kara da cewa, amma duk da hakan akwai tulin abubuwan da ya dace a yi domin cimma manufar kawo karshen cutar a matsayin cutar da ke barazana ga lafiyar al’umma.
Ya ce kaso 58 cikin dari na mutanen Nijeriya da ke fama da cutar mata ne, yayin da kuma maza suka kwashi kaso 42 a cikin dari.
Dakta Aliyu ya ce matakin daukan cutar kai tsaye daga jikin uwa zuwa jariri na da kaso 22 cikin dari, inda Nijeriya take mataki na 30 cikin 100 na gibin kariya daga daukan cutar daga jikin uwa zuwa jariri kai tsaye a fadin duniya.
Ya ce, taken taron na bana na da matukar muhimmanci ‘Al’ummomi: jagoranci zuwa kawo karshen cutar kanjamau nan da karshen shekara 2023’ domin jawo hankalin shugabanni daga bangaren maza da mata da sauran bangarorin mutane wajen daukan matakan kariya daga kamuwa ko yaduwar cutar kanjamau a tsakanin al’umma.
Ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su saka azama wajen yaki da cutar, inda ya ce, “Da hadin kan masu ruwa da tsaki za a iya rage kaifin cutar da kuma saukaka hanyoyin magance cutar a tsakanin al’umma gami da shawo kan gangancin kamu da cutar a tsakanin jama’a.”
Shugaban kwamitin yaki da cutar kanjamau ta majalisa, Amobi Ogah ya ce, majalisar kasa za ta yi kokarin ganin an ware kaso mai tsoka domin yaki da cutar kanjamau a kasar nan.