Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya ce matsalar tattalin arzikin Naijeriya a yanzu ta samo asali ne daga jinkinta cire tallafin mai fiye da shekaru goma da suka wuce, wanda a yanzu ‘yan Nijeriya suke dandana kudarsu sakamakon wannan jinkiri.
Sanusi ya yi wannan bayani a ranar Talata a taron Odford Global Think Tank Leadership.
Tsohon gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa Nijeriya na iya gujewa tsananin hauhawar farashi da matsanancin yanayin tattalin arziki na yau idan da an bari gwamnatin tsohon shugaba kasa, Goodluck Jonathan ta kawo karshen tallafin mai a shekarar 2011.
“Da ‘yan Nijeriya sun barin gwamnatin Jonathan ta cire tallafin mai a shekarar 2011, tabbas za a ji radadi. Amma wannan radadin zai kasance karami daga abin da muke fuskanta a yau. Wannan shi ne dalilin jinkirin,” in ji shi.
A cewarsa, CBN ta riga ta tantance yiwuwar tasirin cire tallafi kuma ta kawo cewa hauhawar farashi ba zai wuce kashi 30 ba idan aka aiwatar da manufar a wancan lokacin.
“A lokacin, mun yi lissafin adadi a Babban Bankin. Na tashi na kafa sharuda bisa ga ka’idodi, inda na ce a cire tallafin yau. Farashin kaya zai tashi daga kashi 11 zuwa kashi 13, zan rage shi a cikin shekara guda. Ba za mu samu hauhawar farashin kaya na kusan kashi 30 ba,” in ji shi.
 
			



 
							







