Fadar shugaban kasa ta sake jaddada aniyar gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu na bai wa duk dan Nijeriya hakkinsa da doka ta tanadar masa musamman a bangaren gudanar da zanga-zangar lumana.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale, a lokacin da yake magana a wani shirin gidan talabijin na TVC a daren Lahadi, ya jaddada cewa, babu wani jami’in gwamnati da ke da hurumin hana ‘yan Nijeriya gudanar da ‘yancinsu na gudanar da zanga-zangar lumana a kowane bangare na kasar.
- An Kama Ɗan Majalisar Jiha Da Wasu Hakimai Kan Zargin Garkuwa Da Mutane A Zamfara
- Zanga-zanga: Za Mu Yi Amfani Da Dandalin Eagle Square Ko Da Izini Ko Babu A Abuja
“Muna kan kujerar shugabanci ne domin jagoranci, ba don mulki da mallakar mutanenmu ba.” In ji Ngelale
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, wasu manyan jami’an gwamnati da sarakunan gargajiya da Malaman addini da kungiyoyi na ta kira da a yi watsi da batun zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da aka shirya yi a fadin kasar a ranar 1 ga watan Agusta.