Hukumar kula da ayyukan kumbo mai dauke da ‘yan sama jannati ta kasar Sin (CMSA) ya ba da labari cewa, ‘yan sama jannati 3 na kumbon Shenzhou-20 sun shiga dakin rayuwa daga dakin tuka kumbon bayan kumbon ya yi nasarar hadewa da tashar sararin samaniya ta Sin.
Da karfe 1 da mintoci 17 na safiyar yau Juma’a ne, ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-19 suka bude kofar dakin rayuwa don maraba da zuwan abokan aikinsu na kumbon Shenzhou-20. Wannan shi ne karo na 6 da ‘yan sama jannatin kasar Sin suka hadu a sasarin samaniya a tarihin sha’anin zirga-zirgar sararin samaniyar kasar, kuma shi ne karo na biyu da shugabanni masu ba da umurni 2 suka sake haduwa da juna a tashar sararin samaniya ta Tiangong bayan shekaru 3 da suka gabata.
Daga baya, ‘yan sama jannatin na runkunonin 2 za su yi karba-karbar aikinsu a tashar, inda za su yi zama tare na tsawon kwanaki 5 don kammala aikinsu cikin hadin gwiwa. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp