Rahotannin da ofishin kula da aikin nazarin sararin samaniya, da kumbo mai dauke da mutane na kasar Sin ya fitar sun nuna cewa, ‘yan sama jannatin da suka kammala aiki cikin kumbo mai dauke da mutane samfurin Shenzhou-14, wato Chen Dong, da Liu Yang, da Cai Xuzhe, sun sauka birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin a asubar yau Litinin 5 ga wata lami lafiya, inda shugabanni da wakilai, na babbar hedkwatar kula da aikin gina tashar nazarin sararin samaniya ta kasar Sin suka tarye su, a filin saukar jiragen sama.
Yanzu haka za a fara gwajin lafiyar ‘yan sama jannatin su uku daga dukkanin fannoni, ta yadda za su samu kulawar da suke bukata. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp