Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Enugu Abubakar Lawal, ya umarci Jami’an tsaro na farin kaya SCID da su gudanar da cikakken bincike kan gobarar da ta tashi a ofishin hukumar zabe da ke a karamar hukumar Igbo-Eze ta Gabas.Â
Gobarar dai ta afku ne da misalin karfe 11 na daren ranar 03/06/2022.
A cikin sanarwar da mai magana da yawun Rundunar, DSP Daniel Ndukwe ya fitar, ya bayyana cewa gobarar ta tashi ne daga bangon wani gini dake makobtaka da ofishin, amma Jami’an kashe gobara ta Jihar sun yi Nasarar kashe gobarar.
In za a iya tunawa dai yankin ya sha fama da hare-haren yan bindiga, inda hakan ya tilasta wa gwamnan jihar, Ifeanyi kakaba dokar hana yawo a kananan hukumomin Igboeze ta Gabas da karamar hukumar Igboeze ta kudu daga karfe 6 na safe zuwa karfe 6 na Yamma .