A ƙoƙarin ta na tabbatar da cewa an hukunta masu maguɗin zaɓe, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bada sanarwar samun nasarar gurfanar da Nasir Idris a kotu, kuma har an yanke masa hukuncin ɗaurin shekara ɗaya a kurkuku.
An ɗaure Nasir ne bayan an same shi da katin zaɓe har 101 A hannun sa.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran INEC, Festus Okoye ya fitar, ya ce an yanke wa Nasir hukunci a Kotun Majistare ta Sokoto.
“An same shi da laifin karya Dokar Zaɓe Sashe na 117 da na 145 na Dokar Zaɓe ta 2002.
“Yan Sandan Jihar Sokoto ne su ka kama shi a ranar 10 ga Oktoba, aka same shi da tulin katin zaɓe har 101, a Ƙaramar Hukumar Sabon Birni, Jihar Sokoto,” inji Okoye.
“Bayan ‘yan sanda sun kammala binciken su, sun aiko mana da fayil ɗin da ke tattare da bayanan da su ka samu. Daga nan kuma INEC ta gurfanar da shi kotu.”
Okoye ya ce a yanzu haka kuma INEC na ci gaba da zuwa shari’ar wani da aka kama da katin zaɓe har guda 367 a Kano. Ya ce hukumar su za ta tabbatar da shi ma wannan ɗin sai an hukunta shi, kamar wanda aka ɗaure a jihar Sokoto.
Idan ba a manta ba, a jihar Kano ‘yan sanda sun Kama wani jigon APC mai suna Aminu Shana, ɗauke da katin rajista har 367.P