Kungiyar kwallon kafa ta AC Milan ta sanar da cewar ‘yan sanda sun nemi afuwa daga Tiemoue Bukayoko, bayan da suka tsayar da shi, suka bincike shi kan zargin harbe-harbe da bingiga a wannan satin.
Lamarin ya faru a birnin Milan ranar 3 ga watan Yuli, inda aka yada faifan bidiyon da ya ja hankalin mutane da yawa a kafar sada zumunta ranar Litinin inda a faifan bidiyon an nuna dan wasan mai shekara 27, wanda ke buga wasannin aro a Milan daga Chelsea, wani dan Sanda na caje shi wasu biyu sun auna motarsa da bindiga sai dai bayan da suka gama binciken dan kwallon tawagar Faransa daga nan suka sallame shi.
Bakayoko ya koma AC Milan kan yarjejeniyar kakar wasa biyu a bara, wanda ya buga wasa a San Siro a kakar wasa ta 2018 zuwa 2019 kuma ya buga wasanni 18 a kakar da ta wuce da Milan ta lashe Serie A.
Dan kasar Faransan dai ya koma Chelsea daga Monaco a shekarar 2017 kan fam miliyan 40, wanda ya buga wa kungiyar Chelsea wasanni 43 a kakar farko sai dai ya koma buga wasa zuwa kungiyar Monaco a watan Agustan shekara ta 2019 kan yarjejeniyar aro, daga nan ya koma buga wasan aro a kungiyar Napoli daga watan Oktoban shekara ta 2020.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp