Kwanaki 4, kafin hukumar zabe INEC ta gudanar da zabukan kujerun gwamna da ‘yan majalisun jihohi, ‘yan takarar kujerar gwamna shida, sun janyewa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jam’iyyar PDP a jihar Adamawa.
Jam’iyyun da ‘yan takaran suka fito sun hada da; Allied People’s Movement (APM) All Progressives Grand Alliance (APGA), National Rescue Movement (NRM), Zenith Labour Part (ZLP), Action Democratic Party (ADP) da Action People’s Party (APP).
Da yake magana lokacin taron ranar laraba a Yola, gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, ya yaba da matakin da sauka mishi da ‘yan takarar suka dauka, yace ba zai daukeshi da wasa ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp