Matashiyar ‘yar kasuwa mai neman na kanta ‘yar Nijeriya mazauniyar Kasar Masar ta bayyana wa shafin Adon Gari, yadda ta rungumi kasuwanci da ci gaban da samu da kuma irin kalubalen da ke fuskanta. Sannan a gefe daya kuma ta bayyana yadda yan uwanta suke taimaka mata wajen tallata hajarta a shafukan sadarwa da sauran kasuwanni, kamar dai yadda za ku ji daga bakinta a cikin tattaunawarsu da BILKISU TIJJANI, ga dai yadda hirar ta kasance
Da fari za mu so sanin cikakken sunanki da tarihinki
Assalamu alaikum, da farko dai suna na Sumayya Gidado Umar wadda aka fi sani da Misis Ay collections, an haife ni a cikin garin Katsina, na yi matarantar firamare a Katsina, haka Sakandire dina ma a cikin Katsina a wata makaranta da ake cewa Alhuda Academy. Wannan shi ne takaitaccen tarihina.
Shin ke matar aure ce?
Eh ni matar aure ce muna zaune a Cairo da ‘ya’yana na biyu ( Zara da Iman)
Malama Sumayya ‘yar kasuwa ce ko kuma ma’aikaciya ce?
A’a ni ba ma’aikaciya bace ‘yar kasuwa ce
Wanne irin kasuwanci kike yi?
Kasuwancin da nake na Abayas ne, takalma, jallabiyyar maza jakukkuna, gaskiya ina saida abubuwa da dama ina turo su daga nan Misra zuwa gida Nijeriya.
Me yaja hankalinki har kika shiga wannan kasuwancin?
Gaskiya abin da ya ja hankalina na shiga sana’a tun ina karama ina sha’awar kasuwancin haka na zo kuma na yi aure mijina shima yana san kasuwancin sosai, duba da duk sauran ‘yan uwana su ma’aikatan Gwamnati ne ya sa na ji ina so ni na gwada yin kasuwancin, duba kuma da baka san yadda rayuwa za ta kasance ba, ba na san kullum na zama me a bani shi ya sa na dage da kasuwancin saboda na rufa wa kaina asiri har ma na taimakawa ‘yan uwana.
Meye matakin karatunki ba?
Matakin karatu na yi difloma a nan Polytechnic Katsina, na kuma yi digiri a nan FCE branch din BUK dake nan Katsina, wannan shi ne matakin karatu na.
Wanne irin kalubale kika taba fuskanta a cikin sana’arki?
A gaskiya na fuskanci kalubale kala-kala musamman farko kasuwancin na duba da bana Nijeriya wasu mutane su kan rike maka kudinka in suka amshi kaya sanin baka da yadda za kai da su ya sa wasu ba sa biya, kalubale kam gaskiya ba laifi akwaishi sai dai mu ce Alhamdulillah, hakan ya sa yanzu in ba biya ka yi ba ko ka ba da wani kaso daga ciki ba ma turo maka da kaya, kalubale na biyu kuma shi ne duba da a intanet muke komai da masu sayen kaya mu kan samu matsala da su wajen amsa sakonninsu, za su yi mana magana saboda yawan mutane ba lallai ne mu amsa musu ba a lokaci daya, hakan zai sa shima masu sayen kaya su yi fushi ko ya fada maka magana, bayan muna kokari ga miji ga yara ga hidimar gida duka dai, to wannan su ne kalubale gaskiya da nake ciki nake fuskanta. Allah ya shige mana gaba.
Zuwa yanzu wadanne irin nasarori kika samu?
To alhamdulillah alhamdulillah gaskiya ba abin da zan ce sai godiya ga Allah, amma kam na samu nasarori sosai mai yawan gaske daga ciki hadda taimakawa na kasa da kai muna godiya ga Allah saosai Alhamdulillah.
Wanne abu ne yafi faranta miki rai game da sana’arki?
Abin da ya fi faranta min rai a sana’a ta shi ne yadda saboda ina jin dadin harka da wasu ya sa nake taimaka masu wajen su bani rabin kudi na cika na sayo masu kaya kafin kaya su zo, su cika su karba kayan su zo su cika su karbi kayan duba da yadda suke farin ciki da wannan abin ya sa a kullum wannan din ya fi komai faranta min rai da yadda suka yadda da ni suke kuma yaba kayan a duk sadda suka amsa wannan sanadiyar hakan ya sa zumunci sosai ya kullu tsakanina da su da har suke zuwa takanas su gaishe da iyayena, wannan abubuwa sun fi komai faranta min rai gaskiya.
Ta wacce hanya kike bi wajen tallata sana’arki?
Yawan hanyar da nake bi su ne zaurukan da na bude a WhatsApp mutane suke ciki nake tallata kayana da kuma sitatus na WhatsApp su instagram su tik tok su ne hanyoyin da nake bi wajen tallata kayana.
Dame kike so mutane su rika tunawa da ke?
Ina so mutane su rika tunawa da ni wajen rikon gaskiya da amana.
Ga gida da yara, ga kuma hidimomin sana’a, shin ta yaya kike samun damar gudanar da hutunki?
Eh to gaskiya abin ba sauki ka hada hidimar iyali ko karatu da kuma sana’a sai ka yi da gaske kuma ka zama jajirtacce, ina hutu ne duk bayan sadda na tura kaya na kan yi sati daya ina hutawa kafin na sake turawa wata oda, wani lokaci din ma na kan yi sanarwa na je hutun sati biyu musamman in an tura kayan da yawa na kan zauna na huta na kula da yara da maigida.
Wace irin addu’a ce idan aka yi miki kike jin dadi?
Addu’ar da na fi jin dadin ta ita ce, Allah ya miki albarka ya albarkaci kasuwancin nan naki ya raya miki zuri’a ya kuma yi musu albarka wannan addu’o’in sun fi komai saka ni na ji dadi gaskiya.
Wanne irin goyon baya kike samu daga wajen iyaye da ‘yan uwanki?
Gaskiya ina samun goyon baya sosai musamman daga wajen iyaye da ‘yan uwana su suka bani shawarwari ko taya ni tallata kayan nawa da kuma hada ni da mutane daban-daban da suke Allah ya saka musu da alheri. Haka zalika kawaye wasu su kan tallata kayan naka ko su hada ka da mutane duka dai gaskiya Alhamdulillah suna bani goyon baya yadda ya kamata.
Me kike fiso cikin kayan sawa da kayan kwalliya?
Abin da na fi so cikin kayan sakawa gaskiya Abaya da leshi, kayan kwalliya kuma Humra da jaka da takalmi.
A karshe wace irin shawara za ki ba ‘yan uwanki mata?
A karshe shawarata ga ‘yan uwana mata ba wai masu aure ba har ‘yan mata da su tashi su nemi na kansu duk wadatar mijinki ba ki san gobe ba don mijinka na da hali ba dalili bane ga mace za ta zauna komai sai kin tambaya ko yana yi kullum kema wata rana za ki so a ce wannan naki ne da kanki kika nema, sannan kina da ‘yan uwa dangi kawaye wani abin za ki yi wa kanki ki ma wasu ma can daban so a tashi a nemi sana’a. ‘Yan mata kuma ko yaya kafin aure ki samu ki fara gina kanki shi kan shi me neman naki zai fi jin dadi in ya ga ba’a zaune kike ba. Allah ya shiga lamarinmu ya bamu sa’a ya sa mu gama da duniya lafiya ya tsare mu ya kare mu daga dukkan abin ki ya shirya mana zuri’a. Amin.