Ministan gidaje da raya birane da karkara na kasar Sin Ni Hong, ya ce yanayin sashen samar da gidaje na Sin ya kara inganta tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025, yayin aiwatar da manufar raya kasa karo na 14, inda jimillar adadin sayar da sabbin gidaje na kasuwa ya kai fadin sakwaya mita biliyan biyar.
Ni Hong, ya bayyana hakan ne a yau Asabar, yayin wani taron manema labarai. A cewarsa, sama da Sinawa miliyan 110 sun amfana daga babban tsarin gyaran tsofaffin gidaje cikin shekarun biyar. Kazalika, tsofaffin gidaje dake unguwanni sama da 240,000 a sassan biranen Sin, sun mori shirin gyaran fuska cikin wa’adin. Don haka gaba daya, yanayin ingancin muhallin biranen Sin ya kara inganta yadda ya kamata. (Mai fassara: Saminu Alhassan)