Sufuri dai abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar dan adam ta fannin zirga-zirga da dakon kaya daga wannan wuri zuwa wancan. Kafin zuwan zamanin kekuna, da motoci da layin dogo da jiragen sama, ana amfani ne da dabbobi kamar rakuma da dawakai da jakuna domin tafiye tafiye da dakon kaya na yau da kullum.
A wancan lokacin, kasar Sin da kasashe da dama sun yi amfani da irin wannan nau’in sufurin a zirga-zirgar da aka fi sani da “silk road’’ wato hanyar siliki domin kasuwanci tsakaninsu.
Daga nan dai aka fara samun ci gaba a yayin da kekuna suka bullo da motoci da sauran ababen hawa.
A yau kamar yadda kowa ya sani, kasar Sin tana kan gaba a sufuri na zamani, kamar irin su layin dogo mai sauri da motoci masu amfani da sabbin makamashi da jiragen sama da filayen jiragen sama na zamani da dai sauransu.
Kamar yadda na lura a ziyarar da na kai a kasar a lokuta daban daban, na fahimta cewa ana ba layin dogo ko kuma jirgin kasa muhimmanci a Sin, a yayinda akwai nau’in layin dogo iri-iri, wanda suka hada da layin dogo mafi sauri wato HSR (ko kuma bullet train) wanda ke da saurin tafiya na kilomita 200-350, da layin dogo na karkashin kasa (metro).
Masana sun nuna cewa a duk fadin duniya, layin dogo shine hanya mafi sauki domin zirga-zirga da dakon kaya. Jama’a da dama dai suna amfani da layin dogo a kasar Sin.
Akwai dai burgewa da ban sha’awa a yayin da na yi amfani da wadannan nau’in layukan dogon yayin da na je larduna da garuruwa a cikinsa, kamar daga Beijing zuwa Shanghai, da Beijing zuwa Nanjing, da Xi’an zuwa Chengdu da dai sauransu.
A duk wannan lokutan, tafiyar tana mai matukar nishadi wanda mutum zai ji kamar yana cikin jirgin sama ne, domin kuwa kirar wannan jirgin kasan tamkar irin na jirgin sama ne, ana dai shafe misalin awa 4 ne kacal a tafiyar kilomita 1,302.
An dai kiyasta jimlar tsawon layin dogo gaba daya a kasar Sin a akan kilomita sama da dubu 150 wanda kuma shi ne mafi tsawo a duniya.
Kamar yadda na ambata, layin dogo na karkashin kasa (metro) ko kuma (subway) akwai shi kusan a duk fadin larduna kasar Sin, jirgin kasa ne mai kayatarwa da ban mamaki ga wanda ya fara ganinsa ko amfani da shi.
Wannan layin dogon dai yana kama da sauran layukan dogo na zamani amma a can cikin karkashin kasa layinsa da tasoshinsa suke. Ana dai amfani da shi ne a zirga-zirga a cikin gari da kewaye. A misali a babban birnin Bejing, yayin da na ziyaci birnin, a ko da wane lokaci zan leka shaguna ko wurin shakatawa ina amfani da shi, domin yana da sauri da arhar tikiti da biyan bukata a cikin lokaci.
A fannin sufurin jiragen sama, kasar Sin ma ba’a bar ta a baya ba, domin kuwa akwai dimbin kamfanonin jiragen sama na fasinja da dama, da kuma filayen jiragen sama na zamani a kowane lardi. Akalla akwai tasoshin jiragen sama kamar 370 a duk fadin kasar.
A cikin tasoshin jiragen sama akwai manya guda biyu a Beijing, wato tashar jiragen sama ta kasa da kasa da kuma Beijing Daxing. Daxing dai sabuwa ce wacce aka gina shekaru uku da suka wuce kuma tafi ko wace tashar jirgin sama girma a duniya, tashar jiragen sama ta zamani ce kuma tana da kyau matuka.
Akwai motocin hawa masu amfani da sabbin makamashi a kasar Sin ma, kuma kasar na gaba a kan tabbatar da an rage amfani da motoci masu tafiya da man fetur ko disel domin kare muhalli don kyautata lafiyar jama’a.
Abin da ya ba ni sha’awa shine irin wadannan motoci suna da lambar lasisi ta musamman, domin duk mota mai amfani da sabbin makamashi kalar lambarta kore ce.
A sakamakon irin wannan ci gaba a fannin sufuri da kasar Sin ta samu kuma ta zama a gaba a duniya, ya sanya Sin tana taimaka ma nahiyar Afirka da kasashe masu tasowa kafa ire-iren wadannan ababen more rayuwa ta hanyar hadin gwiwa.
A misali, a Najeriya, a karkashin hadin gwiwa da kasar Sin, an samu gina hanyoyin layin dogo, da tasoshin jiragen sama da hanyoyin mota da tasoshin jiragen ruwa.
Wadannan ababen more rayuwa ta fannin sufuri dai suna da muhimmanci a rayuwar dan adam da ci gaban tattalin arzikin ko wace kasa.
– Lawal Sale