Bayar da ikon cin gashin kan kananan hukumomi a Nijeriya na ci gaba da fuskantar koma-baya duk da hukuncin kotun koli na bai wa kananan hukumomi kudadensu, sabbin matsaloli sun kunno kai, wanda ya kawo tsaiko wajen aiwatar da wannan hukunci.
Bukatar baya-bayan nan da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi wa kananan hukumomi na su gabatar da bayanan kudaden da aka tantance na shekaru biyu kafin su karbi kason su kai tsaye, wani shingen hanya ne a wannan fafutuka.
- An Nemi Gwamna Mutfwang Ya Yi Takatsantsan Da ‘Yan Barandar Siyasa
- MOFA: Ya Kamata Amurka Ta Daina Siyasantar Da Batun Gano Inda COVID-19 Ta Bulla
Lamarin dai ya ta’allaka ne a kan turjiya daga hukuncin kotun kolin ta amincewa da raba kudaden shiga kai tsaye ga kananan hukumomi. Yayin da ake sa ran hukuncin zai kawo karshen katsalandan din da gwamnonin jihohi suke yi wajen bai wa kananan hukumomi ikon sarrafa kudadensu a matsayin babbar hanyar siyasa.
A tarihance, gwamnonin jihohi suna da gagarumin iko a kan kananan hukumomi ta hanyar gudanar da asusun hadin gwiwa tsakanin jihohi da kananan hukumomi, wanda a lokuta da dama yakan ke haifar da karkatar da kudade ko jinkirtawa, wanda hakan ya sa kananan hukumomin ke fafutukar sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya dora musu. Yanzu, duk da hukuncin da kotun koli ta yanke, wasu gwamnonin suna bin hanyoyin doka don ci gaba da rike kudaden kananan hukumomi.
Sabon koma-bayan ta taso ne lokacin da ake bukata na tantance kudi na tsawon shekaru biyu, wanda ya sanya shakku kan fara rabon kai tsaye nan take. Yawancin kananan hukumomi ba su yi aiki a matsayin masu zaman kansu ba shekaru da yawa, zai musu wahala su samar da takaddun da suka dace a cikin lokaci kafin su iya bai wa kwamitin rarraba asusun tarayya.
Wata majiya daga CBN ta bayyana cewa idan ba tare da cikakken tantance kudi ba, babban bankin ba zai iya bude sabbin asusu ga kananan hukumomin ba.