Abokai, yau na zana wani Cartoon dangane da harbe-harben bindiga da suka yi ta faruwa a kasar Amurka, kuma da hakan ina nuna alhini ga yaran da suka rasu sakamakon harbe harben bindiga da suku rutsa da su a Amurka, musamman ma yara 19 da suka rasa rayukansu kwanan baya a jihar Texas na kasar.
‘Yancin mallakar makamai na samar da sauki ga masu aikata laifuka a kasar, matsalar da ta addabi yaran kasar sosai.
Bai kamata irin wannan matsala ta bullo a cikin wata kasa dake ikirarin kare hakkin Bil Adama da martaba dimokuradiyya ba. Dole ne ‘yan siyasa da masu jarin hujja su farka, kada su jefa yara a cikin tsoro, da nuna rashin kulawa da su.
Da fatan wadannan yaran da suka rasu za su huta cikin kwanciyar hankali a aljannar da babu fitar harsasai a cikin ta. (Mai zana: MINA)