A yanki mai tsaunuka na Qinghai-Tibet, an kafa sansanonin albarkatun tagulla guda hudu da za su iya daukar biliyoyin tan, kuma ana hasashen samun albarkatun tagullar da za su kai tan miliyan 150 a yankin.
Sakamakon haka, ana iya cewa, yanki mai tsaunuka na Qinghai-Tibet zai zama sansanonin albarkatun tagulla masu daraja na duniya, tare da kawo sauyi a tsarin bincike da bunkasa albarkatun tagulla.
Cibiyar nazarin yanayin kasa ta kasar Sin ta fitar da alkaluma yau Litinin, inda ta ce, tun bayan aiwatar da wani sabon zagaye na aikin gano albarkatun ma’adinai, kasar ta ci gaba da kara kokarinta na neman albarkatun tagulla, ta hanyoyin gudanar da ayyukan jin dadin jama’a, da bunkasa sabbin fasahohi, da kuma inganta hadin gwiwa tsakanin gwamnatoci da kamfanoni.
Tuni dai aka riga aka samu babban sakamako wajen neman cin gajiyar albarkatun tagulla a yankin Qinghai-Tibet, da lardin Heilongjiang da sauran yankuna, inda sabbin albarkatun tagulla da aka samu suka ninka adadin da aka samu a lokacin gudanar da shirin aikin na shekaru biyar a karkashin kashi na 13. (Safiyah Ma)