Shugaban yankin Zanzibar na kasar Tanzania, Hussein Ali Mwinyi a ranar Asabar din da ta gabata ya karrama mambobi 21 na tawagar likitocin kasar Sin da lambar yabo, saboda hidimar aikin jinya da suka bayar na tsawon shekara daya a tsibirin na Zanzibar.
Mwinyi ya shaida wa tawagar likitocin na kasar Sin yayin da yake ban kwana da su a gidan gwamnatin Zanzibar cewa, ana da dalilai masu tarin yawa na mika godiya ga irin gagarumin aikin da likitocin kasar Sin suka yi na tabbatar da cewa, jama’ar Zanzibar sun samu hidimar ayyukan kiwon lafiya mafi kyau a cikin shekara guda da ta gabata.
Ya bayyana cewa, tawagar likitocin kasar Sin, sun samar da hidima fiye da jinyar mutane. Haka kuma tawagar ta samar da kayan aikin jinya da magunguna, baya ga horar da ma’aikatan lafiya dake yankin.
Shugaba Mwinyi ya godewa kasar Sin, kan yadda ta tura tawagogin likitoci zuwa yankin, yana mai cewa, tawagogin likitocin kasar Sin, sun taimaka wajen karfafa tsarin kiwon lafiyar kasar tare da ceto rayukan daruruwan mutane.
Tun bayan zuwan tawagar likitocin kasar Sin ta 31 Zanzibar a cikin watan Satumban da ya gabata, tawagar ta samar da hidimar jinya ga majinyata fiye da 6,000 a tsawon shekara guda da ta shafe tana wannan aiki. (Ibrahim)