Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ogun sun cafke wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, wadanda suka yi artabu da jami’an tsaron bayan sun yi garkuwa da wasu ma’aurata a kauyen Bisodun da ke karamar hukumar Obafemi-Owode a jihar Ogun.
Rundunar ‘yan sanda da mafarauta ne suka samu nasarar cafke masu garkuwar wadanda aka bayyana sunansu da Mohammed Bello da Mohammed Bashiru a wani dajin da ke kusa da kauyen da sanyin safiyar Laraba.
LEADERSHIP ta rahoto cewa wadanda ake zargin a ranar Talata da yamma da misalin karfe 8 na dare suka mamaye kauyen Bisodun inda suka yi nasarar tafiya da wasu ma’aurata zuwa cikin dajin da ke kusa da kauyen.
Bayan sace ma’auratan, an ce mutanen kauyen sun aike da sakon neman agajin gaggawa ga ‘yan sandan da ke hedikwatar shiyya ta Owode Egba, inda daga bisani jami’an suka hada tawagar ‘yan sanda da mafarautan yankin domin tunkarar masu garkuwa da mutane a dajin.
A yayin da suke tsakar dajin, ba zato ba tsammani, masu garkuwar suka bude wa tawagar jami’an wuta inda jami’an da mafarautan suka mayar da martani mai inganci nan take.