Rundunar ‘yansandan jihar Neja ta kama wasu mutum biyu bisa zarginsu da hannu a kisan Sarkin kauyen Gusasse, Malam Abubakar Yahaya tare da garkuwa da diyarsa zuwa wani wajen da ba a sani ba.
Jami’in watsa labarai na hukumar ‘yansandan jihar (PPRO), Wasiu Abiodun, ya ce, a kwanakin baya ne wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka farmaki kauyen Gusasse ta Maikunkele da ke karamar hukumar Bosso a jihar Neja tare da tafka ta’asa.
Ya yi bayanin cewa a lokacin da maharan suka kai farmakin, sun harbe basaraken kauyen tare da yin garkuwa da ‘yarsa sannan sun mamaye gidansa da ke Barkuta.
Ya kara da cewa, sun kuma shiga Sabon-Gari da ke Beji inda a nan ma suka harbe wani mai suna Manir tare da yin garkuwa da wani mai suna Alhaji Hassan Gusasse.
Abiodun ya kara da cewa bayan faruwar lamarin, ‘yansanda sun kaddamar da bincike inda suka samu nasarar taso keyar mutum biyu.
Ya ce, wadanda aka kama bisa zargi da hannuna lamarin sun hada da Risku Suleiman dan shekara 34 a duniya, Haruna Umar dan shekara 20 a duniya dukkaninsu mazauna kauyen Kupa da ke Garatuna kan hanyar Bida ta jihar Minna.
A cewar Kakakin ‘yansandan, wadanda ake zargin sun amsa laifukansu Kuma sun karbi naira miliyan 1.5 a matsayin kudin fansar yarinyar basaraken da suka sace, Kuma sun karbi irin wannan kudin a kan Alhaji Hassan Gusasse kafin sake shi.