Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta ce ta ceto mutane bakwai daga hannun musu garkuwa a wasu hare-hare guda biyu da aka yi a kananan hukumomin Bena-Mairai da Ruwan Kanwa, Danko Wasagu da Jega na jihar.
Da yake yiwa manema labarai karin haske game da lamarin a hedikwatar ‘yan sanda da ke Birnin-kebbi, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ahmed Magaji Kontagora, ya ce ‘yan bindigar sun tsare hanyar Bena-Mairarai a unguwar Danko-Wasagu da ke jihar, da samun labarin muka tura jami’anmu wurin, bayan musayar wuta, an yi nasarar kubutar da mutane Ukun da aka yi garkuwa da su ba tare da sun samu wani rauni ba, sune: Jamila Ahmad, Shamsiya Ahmad da Tasi’u Haruna duk daga kauyen Mairairai.
Ya ce an kuma kwato wata mota kirar Toyota Corolla mai lamba Kano DTF 236 LP mallakin ‘yan bindigan, sannan kuma “an kara tsananta tsaro a yankin domin dakile wani kai harin daga ‘yan bindigar ”.
A wani bangaren kuma, kwamishinan ya ce, jami’an tsaro sun kuma ceto wasu mutane hudu da aka yi garkuwa da su a yankin Jega da ke jihar.