Rundunar ‘yansanda Jihar Ebonyi, ta ce ta gano wasu ababen fashewa, biyo bayan abin da ta danganta a matsayin babbar masana’antar da ake yin bama-bamai da tsagerun Biyafara (IPOB) ke yi a Kudu Maso Gabas.
A cewar rundunar bam din na da karfin da zai iya rusa gine-gine da lalata duk wani abu.
- ‘Yan Daba Sun Tarwatsa Taron APC, Sun Yi Awon Gaba Da Shugaban Matasa A Delta
- CMG Ya Fitar Da Shirin “Shawarar Daukar Matakin Neman Bunkasuwa Na 2022” A Shafin Yanar Gizo
An dai gano masana’antar a yankin Obegu da ke makwabta da kananan hukumomin Onicha-Isu da Ishielu da ke jihar.
Kakakin rundunar ‘yansanda, SP Chris Anyanwu, ya bayyana hakan a yau Alhamis a taron manema labarai a garin Abakaliki, inda ya ce bayan rundunar ta samu bayanai a kan masana’antar, ta tura kwararrun jami’anta zuwa gurin, inda ya ce, bama-baman sun kai karfin rusa gine-gine da kuma hallaka mutune.
Ya ce, an yi amfani da manyan sinadarai wajen hada bama-bamai, inda ya kara da cewa, jami’an sun kuma gano wasu kaki mallakar ‘yan kungiyar.
Anyanwu ya ce, jami’an sun kuma kama wani Kwamandan kungiyar Sunday Ubah, inda ya ce, a lokacin samamen ‘ya’yan kungiyar sun kuma harbi wasu daga cikin jami’an ‘yansandan da aka tura
Ya ce, jami’an sun kuma samu nasarar kashe biyu daga cikin ‘ya’yan kungiyar, inda kuma wasu suka arce dauke da harbin albarusai a jikinsu.