Rundunar ‘yansanda reshen jihar Sokoto ta kama wani Kabiru Abubakar da ake zargi da kware wajen satar babura.
Kakakin rundunar, ASP Ahmad Rufa’i, a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, ya ce an kama Abubakar ne bayan ya saci wani babur da aka a ajiye a harabar asibitin koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo, UDUTH da ke Sokoto.
- Nan Ba Da Jimawa Ba Makiyaya Za Su Ci Gaba Da Jigilar Dabobbi A Jirgin Kasa – NRC
- Ganduje Da Mai Dakinsa Za Su Gurfana A Gaban Kotu A Kano
“Rundunar ‘yansandan jihar Sokoto ta kama wani Kabiru Abubakar mai shekaru 25 bisa zargin satar babur a asibitin koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoto, UDUTH, a ranar 5 ga Yuli, 2024.
“An gano babur din ne bayan da aka kama wanda ake zargin, yayin da mai babur din ya gano kayansa kuma ya bayyana cewa nasa ne,” in ji Rufa’i.
Kakakin ‘yansandan ya kara da cewa, wanda ake zargin wanda ya amsa laifin ya kuma bayyana cewa ya kuma sace babur daya a Rahamat Clinic Sokoto mallakar wani Naziru Muhammad da ke kan titin Kano Rod.
“Ya bayyana cewa, Kabiru Alhaji Yaro na Unguwar Bello Way, Sokoto a matsayin wanda ke amsar baburan, binciken da aka gudanar ya kai ga gano babura shida,” in ji Kakakin Rundunar