Rundunar ‘yansandan jihar Katsina ta ce ta kama wasu mutane 72 da ake zargi da satar wayar salula, wadanda akafi sani da Kauraye, da ke tada hankulan Al’umma a babban birnin jihar Katsina.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan (PPRO), CSP Gambo Isah ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Katsina.
Ya ce an kama wadanda ake zargin ne a wurare daban-daban a cikin garin Katsina bayan da rundunar ta kai farmaki maboyarsu.
Isah ya ce yankunan da ‘yansandan suka kai farmakin sun hada da Sabuwar Unguwa, Gadar Nayalli, Modoji, Tudun ‘Yan Lihida da kuma Kwabren Dorawa.
Sauran yankunan sun hada da Janbango, Abattoir, Filin Canada, Lambun Dankwai, Kofar Marusa, Tsalawa, da Chake, da dai sauransu.
“Rundunar ta na mika godiyarta ga jama’a bisa goyon bayan da suke baiwa ‘yansanda da sauran jami’an tsaro a jihar.
“Rundunar ‘yansandan ta umurci jama’a da su kai rahoton duk wani mutum ko wata kungiya da suka yi zargi ga ‘yansanda ta layukan gaggawa na ‘yan sandan kamar haka: 08156977777, 09053872247.”