Rundunar ‘yansandan Nijeriya reshen jihar Kebbi ta kama wasu manyan motoci guda biyu dauke da kwantena mai tsawon mita hudu zuwa hudu, mai dauke da lambobi T-21608 LA, T- 21520 LA duk lambar Legas da ke dauke da damtse na taba wiwi da ake zargin tabar wiwi ce a kan iyakar jihar Kebbi da Jamhuriyar Benin, a gundumar Maje- Tsamiya ta karamar hukumar Bagudo ta jihar.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar PPRO SP Nafi’u Abubakar, ya bayyana hakan a lokacin da ta kira taron ganawa da manema labarai a hedikwatar ‘yansanda a ranar Alhamis a Birnin Kebbi.
Ambaliyar Ruwan Sama Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutum 3 A Jihar Kebbi
Kakakin rundunar ya ce, jami’an hukumar ‘yansandan jihar Kebbi da ke aiki da rundunar jihar, sun kama motocin biyu ne a ranar 10 ga watan Satumba, 2023 a Maje-Tsamiya a karamar hukumar Bagudo ta jihar. Yana mai jaddada cewa bayan binciken manyan motocin guda biyu da ke shake da batar wiwi dauri 4,927, sai kuma harsasai masu rai 7,500 da kuma wasu fakiti 4,906 na damtse na bata wiwi duk an gano su a cikin motocin guda biyu.
Kazalika ya kara da bayyana cewa, motar ta farko an kama ta ne dauke da daurin bata wiwi guda 4,927 da aka damke wasu mutane uku, direta da wasu mutane biyu: Emmanuel Chukwuma na karamar hukumar Bende, jihar Abia, Kanta Bisa karamar hukumar Asaka, dan kasar Ghana da kuma Shola Adeyemi na karamar hukumar Olufan, karamar hukumar Akure, jihar Ondo duk a cikin mota daya ta taho daga Ghana zuwa Togo zuwa jamhuriyar Benin sannan ta wuce iyakar Nijeriya ta karamar hukumar Bagudo ta jihar Kebbi.
Har ilayau, an kama motar ta biyu dauke da fakiti 7,500 na daurin bata wiwi da kuma harsashi 4,906 da kuma direban Abdulrazak Agboola na Unguwar Iyana-Ajiya a Ibadan, jihar OYO, amma wasu da ake zargin tare da shi yayin binciken motar sun tsere, amma rundunar ‘yansanda za ta gano su don tabbar da cewa an kama su nan ba da jimawa ba.
Ya kuma ce ana gudanar da bincike kan lamarin kuma nan ba da dadewa ba za a kama wasu jiga-jigan da suka gudu, bayan bincike rundunar za ta aiwatar da matakan da suka dace. Duk yawan na bata wiwi da aka kama tana Naira miliyan 600 a kiyasi.
A wata hira da ya yi da manema labarai, direban babbar motar ta farko, Emmanuel Chukwuma, ya ce ya dauki katan-katan abubuwan sha daga Legas zuwa Ghana a kan hanyarsa ta dawowa, an ba shi kwangilar daukar daurin bata wiwi guda 4,927 da zai kai garin Legas kan kudi Nair dubu dari hudu.
Ya kara da cewa an ba shi Naira dubu dari a matsayin kamun cinike, idan ya sauke kayan sai a biya shi sauran dubu dari, kuma daga Ghana zuwa iyakar Nijeriya ya wuce cikin nasara. Amma da ya isa kan iyakar Nijeriya inda ya ce na wuce wasu shingayen jami’an tsaro guda tara, amma na yi rashin sa’a tawagar ‘yan sandan da ke sintiri a kan iyaka suka tare motar suka mayar da ni maje-Tsamiya da ke karamar hukumar Bagudo inda suka yi bincike kan motar suka samu daurin bata wiwi shake da motar.
Ya ci gaba da cewa bayan haka an kama shi tare da wasu mutane biyu a cikin motar, daga nan aka dauke su zuwa babban ofishin bincike na SCID a hedikwatar ‘yansanda da ke Birnin Kebbi har da motar.
Hakazalika, direban manyan motoci na biyu, Abdulrazak Agboola daga Ibadan Oyo, ya bayyanawa manema labarai a rundunar ‘yansanda cewa, yana Ibadan ne aka kira shi ta wayar tarho daga jamhuriyar Benin cewa suna bukatar ya zo jamhuriyar Benin ya tuka babbar mota zuwa Akure, jihar Ondo akan kudi Naira dubu dari biyu amma bayan an sauke batar wiwi din, amma bai yi sa’a ba, inda aka kama shi da daurin bata wiwi guda 4,906 da kuma harsashin bindiga guda 7,500. Yanzu haka ina cikin ga hannun ‘yansanda, yayin da suke gudanar da bincike kan lamarin.
Ya ce mutanen da suka dauke ni kwangilar tuka mota sun gudu ne a lokacin da jami’an ‘yansandan da ke sintiri a kan iyakar, a yayin da suke binciken motar suka bar ni. Yanzu ina hannun ‘yansanda.