Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta kama wasu mutane 157 da ake zargi tare da kwato tarin muggan kwayoyi, bindigu, da kuma wasu kayayyaki da aka sato a wata gagarumar shara da ta ke yi a jihar.
Aikin wanda ya dauki tsawon makwanni hudu yana daga cikin kokarin sabon kwamishinan ‘yansanda, CP Ibrahim Bakori wanda ya fara aiki a ranar 17 ga Maris, 2025.
- Batawa Sin Suna Ba Zai Taimaka Kawar Da Tambarin Amurka A Matsayin Daular Kutsen Intanet Ba
- “Kafafen Sada Zumunta”, Yanzu Sun Zama Ƙungiyar Ta’addanci, In Ji Sarkin Musulmi
Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Laraba, CP Bakori ya ce, daga cikin wadanda aka kama har da wasu mutane uku da aka kama da bindigogi kirar guda 19 da kuma harsashi 114.
Bakori ya ce, makaman da ake zargin an dauko su ne daga jihar Filato, ana shirin kaddamar da wani mugun nufi ne acikin Kano da kuma jihohin da ke makwabtaka da ita.
Ya kara da cewa, bisa ga sahihan bayanan sirri, jami’an sun kai samame a wata maboya da ke Kuntau da Gwale, inda suka bankado yadda kungiyar ke gudanar da muggan ayyukanta.
A wani samame da jami’an ‘yansandan suka gudanar sun kama wata babbar mota makare da buhunan siminti amma kuma an boye kwalaye shida wanda ake zargin kwayar tramadol ce da kudinsu ya haura Naira miliyan 150.
An kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu akan safarar kwayar da aka dauko daga Sokoto zuwa jihar Jigawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp