Jami’an rundunar ‘yansandan jihar Neja sun kama wasu masu mutane 6 masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a wani wurin da ake hakar ma’adanai da ke kauyen Dangado a karamar hukumar Paikoro a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansanda (PPRO) a jihar, Wasiu Abiodun, ya ce kamen ya biyo bayan sahihan bayanai.
Abiodun ya ce rundunar ‘yansandan ta ta kai farmaki wurin da ake hakar ma’adinan inda suka yi artabu da masu hakan ma’adanai da ke dauke da muggan makamai.
A yayin samamen, kakakin ‘yansandan Neja ya ce an kama mutane shida a wurin da ake hakar ma’adinan yayin da wasu kuma suka tsere.
Abiodun ya bayyana sunayen wadanda ake cafken da Aliyu Rabiu, Samaila Ibrahim, Sadiku Auwal, Ibrahim Babangida, Musa Adamu da Sani Hassan.