Rundunar ‘yansanda a birnin tarayya Abuja, ta ce ta kama wasu mutane 15 da ake zargi da lalata wani rumbun ajiyar kaya na hukumar raya babban birnin tarayya Abuja.
Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sanda a birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi a Abuja.
- Wasu Mazauna Abuja Sun Shiga Rumbun Ajiya Na Hukumar NEMA Sun Sace Kayan Abinci
- NEMA Ta Musanta Mallakar Wani Rumbun Ajiyar Abinci Da Aka Wawashe A Abuja
Ta ce, wasu jami’an tsaro biyu da jami’an kula da rumbunan da ke aiki a wurin suna daga cikin wadanda ake zargin kan barna a rumbun ajiyar da ke unguwar Tasha a Abuja.
Adeh ta ce an kwato buhunan masara guda 26 da Babura biyar da kuma wasu kwanukan rufi na aluminium daga hannun wadanda ake zargin.
“Rundunar ‘yansanda a birnin tarayya Abuja ta samu rahoto game da harin da aka kai a unguwar Tasha da ke Abuja, a ranar 3 ga Maris.
“Harin ya haifar da barna tare da wawashe kayan ajiyar da ke wurin.
Sashen bunkasa noma da raya karkara na FCTA, ya tabbatar da sace kaya a ma’ajiyar a ranar Lahadi.