Jami’an rundunar ‘yansandan jihar Bauchi sun kama wasu mutane biyu bisa zarginsu da hannu wajen satar wata koriyar mota kirar Honda Civic-2000 a Yelwan Tudu da ke wajen birnin Bauchi.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, kakakin rundunar ‘yansandan Bauchi, CSP Ahmed Wakil, ya ce wadanda ake zargin sun sace motar ne mai lamba ALK-627-GG inda aka ajiye ta a kasuwar Yelwan Tudu.
- Kyautar LEADERSHIP Ta Kara Zaburar Da Mu Kan Sauke Nauyin Al’ummar Jigawa Akanmu – Gwamna Namadi
- Hafsan Soji Ya Gana Da Shugabanni A Filato Kan Hare-haren Da Suka Yi Ajalin Mutane
Ya bayyana wadanda ake zargin Ibrahim Uzeru dan shekara 30 mazaunin Kashere Santuraki da ke karamar hukumar Akko a jihar Gombe da kuma John Paul dan shekara 35 mazaunin Bayan Gari a Bauchi.
CSP Wakil ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin bayan kammala bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp