Rundunar ‘yansandan Jihar Kano ta kama wasu mutane uku dauke da takardun kudi jabu fiye da Naira biliyan 129 wanda suka hada da Dalar Amurka da Sefa Naira.
Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai, inda ya ce, “kudaden jabun sun hada da dala miliyan 3,366,000 da Sefa miliyan 51,970,000 da kuma naira miliyan 1,443,000.
“Wanda aka kama da kudin da kuma wajen wanda ake zargin sun samu kudin duk suna tsare a hannun hukumar, kuma in an gama bincike za a gabatar da su a gaban kotu”.