Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta cafke wani mutum mai shekaru 35 da haihuwa bisa zargin kashe wata matar aure ‘yar shekara 22 mai suna Rumaisa Haruna.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar (PPRO) ya fitar a ranar Talata, SP Haruna Kiyawa, ya ce wanda ake zargin Shu’aibu Abdulkadir na unguwar Madatai a Kano, an kama shi ne a ranar 23 ga watan Mayu, bayan shafe makonni ana gudanar da bincike.
- Abacha Ya Shirya Kashe Ni, Abiola Da Yar’Adua A Gidan Yari – Obasanjo
- Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Amso Bashin $21.5bn Da ₦757.9bn
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, an samu Rumaisa ne a gidan aurenta da munanan raunuka a wuyanta a ranar 6 ga Afrilu, 2025, a Tsamiyar Duhuwa da ke unguwar Farawa a Kano.
Mijinta mai suna Ibrahim Mohammed ne ya gano ta, inda aka garzaya da ita asibiti, daga bisani aka tabbatar da mutuwarta.
“Wanda ake zargin ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa, inda ya amince da haurawa cikin gidan matar, inda ya shake ta, sannan ya daba mata wuka a wuya, wanda ya yi sanadiyar mutuwarta.
Sanarwar ta kara da cewa “Za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp