Rundunar ‘yansanda sun yi nasarar kama wani matashi mai suna Muhammad Ismail dan shekaru 30 da buhunan tabar Wiwi 45 da wasu kwayoyi a karamar hukumar Malunfashi ta jihar Katsina
Da yake yi wa manema labarai jawabi, kakakin rundunar ASP Abubakar Sadiq Aliyi ya bayyana cewa sun samu wannan nasara ne ta hanyar samun bayanan sirri.
- Wace Alkibla Taron Magance Shan Kwaya Na Katsina Ya Dosa?
- Kotu Ta Umarci Gwamnatin Tarayya Ta Biya Emefiele N100m Kan Tsare Shi Ba Bisa Ka’ida Ba.
Ya Kuma kara da cewa wanda ake zargin mai suna Muhammad Ismail Dan shekaru 30 yana zaune ne a unguwar B.C.G.A a garin Malunfashi ta jihar Katsina
“lokacin da jami’an mu suka samu labari ba su yi kasa a gwiwa ba, inda nan take baturen ‘yansanda na Malunfashi ya hada jami’an mu domin kama wadanda ake zargi.” Inji shi
A cewar ASP Abubakar Sadiq Aliyu an kama wanda ake zargi da buhunan tabar wiwi guda 45 da kwalabe 500 na kayan maye da kwaya mai suna D5 duk a tartare da shi.
Haka kuma ya yi bayanin cewa a lokacin da suke gudanar da bincike wanda ake zargi Muhammad Ismail ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa inda har ya ambaci sunan wani mutum Ibrahim Kisko a matsayin abokin sana’arsa wanda yanzu haka rundunar na nemansa ruwa a jallo.
“Yanzu da zaran mun kammala wannan taro na manema labarai zamu mikawa hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA tare da kayayyakin da aka kama domin cigaba da bincike akan lamari” inji ASP