Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta kama wasu mutane uku da ake zargin ‘yan damfara ne da suka damfari wani tsabar kudi har Naira Miliyan N1,030,000 ta hanyar ba saja da jami’an tsaro.
Wadanda ake zargin sun hada da Nasiru Adamu mai shekaru 30 daga jihar Sokoto; Yusuf Sani, 49; da Aliyu Yusuf dan shekaru 25, dukkansu daga karamar hukumar Daura ta jihar Katsina, an kama su ne a ranar 2 ga Satumba, 2025, da misalin karfe 1:30 na rana a unguwar Dan’agundi ta Kano.
- Harin Sojojin Sama Ya Hallaka Ƴan Ta’adda 15 A Borno
- Ƴan Siyasar Arewa Na Rigima Da Juna, Tinubu Na Murna — Jibrin
Kakakin Rundunar, Abdullahi Kiyawa, a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Alhamis, ya bayyana cewa kamen ya biyo bayan kiran gaggawa daga wanda aka damfara, mai suna, Salisu Ibrahim.
Kakakin ‘yansandan ya ce, binciken farko da aka yi ya nuna cewa wadanda ake zargin sun bayyana kansu ne a matsayin jami’an tsaro kuma sun yi ikirarin cewa suna da kwarewa ta musamman don taimaka wa wanda aka damfarar.
Ya kara da cewa wadanda ake zargin sun umurci Ibrahim da ya kawo kudin zuwa wani wuri inda suka yi alkawarin taimaka masa.
Ya kara da cewa jami’an ‘yansanda tare da hadin gwiwar jama’a sun yi nasarar cafke duk wadanda ake zargin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp