Jami’an ‘yansanda tare da hadin gwiwar ’yan kungiyar mafarauta a jihar Bauchi, sun yi nasarar kashe wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne su takwas a wani artabu da suka yi a kan iyakar jihar Bauchi da Filato.
LEADERSHIP ta samu cewa, a yayin artabun, rundunar ‘yansandan ta kuma ceto kimanin mutane uku da aka yi garkuwa da su.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Bauchi, SP Ahmed Wakil ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Bauchi a ranar Alhamis.