Rundunar ‘yansandan Nijeriya a jihar Katsina ta ce jami’anta sun yi nasarar kashe wasu Shugabannin ‘yan bindiga uku a jihar.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Aliyu Abubakar Musa ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan (PPRO), Abubakar Sadiq Aliyu, ya fitar a ranar Talata.
- ‘Yansanda Sun Yi Barazanar Sa Kafar Wando Daya Da Masu Yunkurin Tada Hargitsi A Kano
- Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Aliyu A Matsayin Gwamnan Sakkwato
Sanarwar ta bayyana cewa, jami’an ‘yansandan a lokacin da suke sintiri na hadin guiwa tare da ‘yan kungiyar ‘yanbanga, sun yi artabu da wasu ‘yan bindiga da suka yi wa rundunar hadin gwiwar kwanton bauna a yankin Kwarare da ke karamar hukumar Jibia ta jihar, amma jami’an suka jajirce wajen mayar da wuta, lamarin da ya tilastawa ‘yan ta’addan guduwa zuwa cikin dazuka.
“A yayin da rundunar ta bi sahun ‘yan ta’addan da suka arce, an gano gawarwakin mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da kuma babur guda daya na ‘yan ta’addan.
“Da ake tantance gawarwakin, an gano wani Bala Wuta, wanda ake zargin shugaban ‘yan bindiga ne da ke addabar karamar hukumar Jibia da kewaye; Dogo Na Sahara, da Hassan Bukuru,” inji shi
Don haka, kwamishinan ya bukaci jami’an da su ci gaba da gudanar da ayyukan share ‘yan ta’addan, yana mai kira ga ’yan jihar nagari da su ci gaba da baiwa jami’an tsaro bayanai masu muhimmanci kuma a kan lokaci game da ayyukan ‘yan ta’addan domin daukar matakin gaggawa don kawo karshen matsalar rashin tsaro.