Rahotanni sun tabbatar da cewa rundunar ƴansanda ta ƙasa ta kashe wasu mutum uku da ake zargin ƴanbindiga ne, waɗanda suka addabi arewacin ƙasar nan.
A cewar ƴansandan, harin da suka kai kan ‘yan ta’addar ya na cikin ƙoƙarin jami’an suke yi na kawo ƙarshen matsalolin rashin zaman lafiya da ya ke damun Nigeriya.
- Hukumar ‘Yansanda Ta Yi Wa Wasu Manyan Jami’anta Karin Girma
- ‘Yancin Gashin Kai: Ma’aikatan Kananan Hukumomi Sun Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki
Mai magana da yawun rundunar ƴansanda ta ƙasa, ACP Olumuyiwa Adejobi ya bayyana cewa, bayan wani shiri da ƴansanda suka yi, a watan nan na Yuli a jihohin Taraba da Filato da Adamawa da Nassarawa da jihar Niger, ƴansandan runduna ta musamman sun samu nasarar kashe wasu ƴanbindiga uku, bayan yin musayar wuta da su.
Ya ce ƴanbindigar sun yi yunƙurin guduwa su bar makamansu amma suka buɗe musu wuta, inda suka kashe wasu kuma suka ji munanan raunika a cikinsu.
Ya ci gaba da cewa, harin da suka kai wa ƴanbindigar ya sa sun samu bindiga ƙirar AK-47 guda goma da aka yi amfani da su wajen yin garkuwa da mutane da fashi da makami da sauran laifuffuka.
Babban sufeton ƴansanda na ƙasa, Kayode Egbetokun ya sake tabbatar da ƙoƙarin rundunar wajen tabbatar da cikakken tsaro a faɗin ƙasar nan ta hanyar samun bayanan sirri daga jami’ansu.
Mai magana da yawun rundunar ƴansandan ya ce rundunar ta duƙufa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin ƙasar nan, sannan ya buƙaci al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro bayanan sirri da goyon baya domin samar da tsaro.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp