Rundunar ‘Yansandan Jihar Delta ta tabbatar da mutuwar wata Ba’amurkiya mai shekaru 60 mai suna Jackueline, wadda aka ruwaito ta rasu yayin da take ziyartar saurayinta a Karamar Hukumar Udu ta jihar.
Mai magana da yawun rundunar, Bright Edafe, ya bayyana cewa an kama saurayin mamaciyar da aka sani da suna Alawode kawai, domin ci gaba da bincike kan halin da ya jawo mutuwarta.
Jaridar Banguard ta ruwaito cewa Jackueline ta iso Nijeriya daga Amurka a ranar 15 ga Satumba domin yin hutu tare da saurayinta. Sai dai an ce ta samu matsalar lafiya bayan ‘yan kwanaki, inda aka garzaya da ita asibiti a Warri, amma likitoci suka tabbatar da rasuwarta tun kafin isowarta.
Rundunar ‘yansanda ta tabbatar da cewa ana gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin musabbabin mutuwarta.