Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta tsaurara sa ido kan tsaro a fadin al’ummomin kan iyaka bayan wani taron bitar dabarun yaki da ta’addanci.
Taron, wanda aka gudanar a ranar Litinin a hedikwatar ‘yansandan jihar da ke Bompai, Kano, ya tattaro Kwamandoji da sauran manyan jami’an rundunar domin sake duba matakan tsaro da ake amfani da su da kuma tsara wasu hanyoyi don kiyaye tsaron jihar.
A cikin sanarwar da mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a madadin Kwamishinan ‘yansanda, ya ce CP Bakori ya yaba wa jami’an kan “jajircewa da kuma hidimar da suke yi wa rundunar da kuma al’ummar jihar Kano. Kwamishinan ya kuma yi nazari kan nasarorin tsaro na baya-bayan nan kuma ya bukaci kwamandojin da su ci gaba da daƙile ayyukan ta’addanci a Jihar”.
Ya bayyana cewa, zaman bitar ya yi daidai da umarnin Sufeto Janar na ‘Yansanda, IGP Kayode Egbetokun, musamman kan karfafawa jami’an rundunar. Don haka, CP Bakori ya umurci Kwamandojin da su zurfafa wayar da kan jama’a a yankunan karkara da birane domin sanar da su irin rawar da suke takawa wajen wanzar da zaman lafiya da daƙile ayyukan ‘yan ta’adda.














