Rundunar ‘yansandan jihar Zamfara ta kafa kwamitin bincike kan yadda wasu ‘yansanda suka kama motar shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Tukur Danfulani, da tsare direbansa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Yazid Abubakar, ya bayyana haka a Gusau babban birnin Jihar Zamfara.
- ‘Yan Sa-Kai Sun Kashe Mutum 6 A Zamfara
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 4 Da Ceto Mutum 24 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Zamfara
A cewarsa, rundunar ba ta da masaniya kan lamarin amma za ta ci gaba da gudanar da cikakken bincike kan wadanda ake zargin.
“Ba mu samu wani rahoto mai kama da haka ba, amma kwamishinan ‘yansanda, Muhammad Bunu, ya gayyaci dukkan bangarorin da abin ya shafa domin gudanar da bincike.
Rundunar ‘yansanda ta mayar da martani ga wata sanarwa da Sakataren yada labaran Jam’iyyar APC na Jihar, Yusuf Idris, ya yi a ranar Lahadi, inda ya zargi cewa wasu ‘yansandan da ke aiki a gidan gwamnati Gusau, sun yi wa direban wulakanci tare da kama shi da tsare shi na sa’o’i.