Mayar da hankali kan taruka biyu na kasar Sin, wato taron majalisar wakilan jama’ar kasar (NPC) da kuma taron majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar (CPPCC), muhimmin abu ne ga manyan shugabannin kamfanonin kasashen waje dake kasar Sin.
Zuwa karshen shekara ta 2024, adadin kamfanonin da baki ’yan kasashen waje suka zuba jari don kafa su a kasar Sin, ya zarce miliyan 1.239. A matsayinsu na wadanda ke gane wa idanunsu, da wadanda ke bayar da gudummawa, gami da wadanda ke cin moriya, daga harkokin yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje na kasar Sin, kamfanonin jarin waje sun riga sun bada hadin-kai tare da samun ci gaba tare da bunkasar tattalin arzikin kasar Sin.
A wajen tarukan biyu da aka gudanar a wannan watan da muke ciki, an bullo da wasu ingantattun manufofi, wadanda suka karfafa gwiwar kamfanonin jarin waje. A cikin rahoton aikin gwamnati na bana, an mayar da “fadada bude kofa ga kasashen waje, da tabbatar da ci gaban cinikin waje da jarin waje yadda ya kamata” a matsayin daya daga cikin muhimman ayyuka 10 na gwamnatin kasar Sin a shekara ta 2025. Tun daga fadada bangarorin da suka shafi sadarwa, likitanci da ilimi, har zuwa karfafa gwiwar masu zuba jari na kasashen waje don su kara zuba jari, da tabbatar da hakkokin kamfanonin waje dake kasar Sin, da kuma inganta yanayin gudanar da kasuwanci a kasar, akwai alamu da dama dake shaida cewa, kasar Sin na habaka bude kofarta ga kasashen ketare, kana, jarin waje na kara fuskantar damarmaki a kasar ta Sin.
Ana ci gaba da bullo da wasu nagartattun manufofi a kasar Sin, al’amarin dake janyo karin damarmaki. Don haka, yanzu lokaci ne mafi dacewa ga kamfanonin jarin waje su gudanar da ayyuka a kasar Sin, inda bangarorin biyu za su ci moriya tare. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp